Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afirka za su ci gaba da samar da alheri ga jamaarsu
2019-06-26 13:09:15        cri

Bayan da aka gama taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC a birnin Beijing na kasar Sin jiya Talata, jami'an bangarorin biyu sun bayyanawa manema labarai ra'ayi iri daya da aka cimma tsakaninsu da nasarorin da aka samu a wajen taron.

Shugaban kwamitin tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC na kasar Sin, wanda kuma shi ne mataimakin ministan kasuwancin kasar, Qian Keming ya bayyana cewa, an amince da hadaddiyar sanarwa kan takardar sakamakon taron kolin FOCAC, da cimma matsaya daya kan matakan hadin-gwiwa a nan gaba, wanda ke nufin tsayawa ga raya kyakkyawar makomar dan Adam ta bai daya, da kara fadada hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin shawarar "ziri daya da hanya daya", da kara bude kofa ga kasashen waje bisa tushen nuna adalci, ta yadda Sin da Afirka za su samar da alheri ga daukacin al'ummarsu baki daya.

Shi ma a nasa bangaren, babban jami'in kasar Senegal, wadda ta jagoranci dandalin FOCAC a madadin kasashen Afirka, kana babban mashawarcin shugaban Senegal kan harkokin kasashen waje, Oumar Demba Ba ya ce, dangantakar abota ta hadin-gwiwar Sin da Afirka, dangantaka ce ta ainihi da gaskiya, wadda bata bukatar tsoma baki daga wasu kasashe, kana Sin da Afirka, suna iya raya zumunci da hadin-gwiwarsu yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China