Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta gabatar da manufar kudi domin daidaita matsalolin da ake fuskanta
2020-04-07 12:33:21        cri

Jiya Litinin, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kira taron manema labarai, inda ta gabatar da manufar kudin kasar domin fuskantar cutar numfashi ta COVID-19. Ministar harkokin kudi, kasafi da tsare-tsare ta Nijeriya Zainab Ahmed ta bayyana cewa, Nijeirya za ta nemi rancen kudi na dallar Amurka biliyan 3.5 daga Asusun ba da lamuni na IMF da bankin raya kasashen Afirka, domin aiwatar da shirin kasafin kudin kasar Nijeriya na shekarar 2020.

A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar za ta samarwa kananan hukumomin kasar dalar Amurka miliyan 150 daga Asusun kasa. Ban da haka kuma, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zartas da shirin gina ababen more rayuwa dake shafar mutane dubu 774, domin samar da Karin guraben aikin yi da kuma raya tattalin arziki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China