Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilai 3 da suka sanya Amurka ta sossoki WHO
2020-04-09 21:08:01        cri

Kwanan baya, manyan jami'an gwamnatin kasar Amurka, sun yi ta sukar hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO. Har ma a wurare da dama, shugaban Amurka da kansa, ya soki WHO da cewa ta bai wa Amurka shawarar da ba ta dace ba a fannin kandagarki da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ya kuma yi barazanar dakatar da kudaden da Amurkar take baiwa hukumar.

A ranar 8 ga watan nan kuma, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya yi shelar cewa, WHO ba ta yi aikinta yadda ya kamata ba, don haka Amurka za ta sake tunani game da bai wa hukumar kudade.

Dangane da wadannan suka da Amurka ta yi, babban daraktan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a ranar 8 ga wata cewa, siyasantar da yaduwar annobar ya yi kama da kashe kai. Ya ce idan ba a son ganin karin gawawwaki, to ya zama wajibi a kawar da siyasa daga harkokin yaki da cutar.

A dai wannan rana, babban sakataren MDD António Guterres, shi ma ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi kira ga kasashen duniya, da su goyi bayan WHO yayin da ake yaki da annobar. Gutterres ya ce kasashen duniya ba su amince da sukan da Amurka ta yi wa WHO ba.

Yanzu haka dai, sakamakon yaduwar annobar ta COVID-19 a yankunan kasashen Asiya, da Afirka, da Latin Amurka, ya sa matsalar karancin albarkatun kiwon lafiya ta kara yin kamari. Kasashe masu tasowa na bukatar taimako. A matsayinta na kasar da ta fi karfi a duniya, Amurka ta mallake kayayyakin kariya daga hannun sauran kasashe, ta kuma hana sayar da marufin hanci da baki ga kasashe makwabtaka. Kana ba ta biya taimakon kudi da yawansa ya kai miliyan 100 ba tukuna, wanda ta yi alkawarin biya a baya.

Yadda Amurka mai ra'ayin nuna bangaranci ta soki WHO, tare da yin barazanar dakatar da kudaden da ya kamta ta baiwa hukumar, zai zamo abu mai hadari, ga hadin gwiwar da ke tsakanin kasa da kasa wajen yaki da annobar, haka kuma zai illata moriyar al'ummomin kasa da kasa, ciki har da Amurkawa.

Kamar yadda shugaban Amurka ya ce, kwayoyin cuta, abokan gaba ne da ba a iya ganin su. Yaki da su, yaki ne mai wahala. Ba za a iya cimma nasarar yakin ba, har sai an hada kai sosai. Kurakuren da gwamnatin Amurka ta yi sun salwantar da rayukan jama'arta, da dukiyoyinsu masu yawa. Abun tambayar dai shi ne, ko Amurkan za ta ci gaba da yin haka? (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China