Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ta hanyar sallamar kyaftin Crozier, mene ne abun da kasar Amurka ke son boyewa?
2020-04-05 17:11:53        cri

Saboda rubuta wata wasikar neman taimako ga magabatansa, don neman kubutar da sojojin dake karkashin kulawarsa daga cutar COVID-19, Brett Crozier, ya rasa mukaminsa na kyaftin din babban jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen saman yaki na USS Theodore Roosevelt. Bisa al'adar kasar Amurka, ya kamata a kalli wannan mutum dake neman kubatar da dubban mutane a matsayin wani jarumi ne. Duk da haka, maimakon a yaba masa, an yanke masa hukunci mai tsanani. To, mene ne dalilin da ya sa haka?

Kafar watsa labarai ta CNN ta ce wasu sojoji 137 dake cikin jirgin ruwan na USS Theodore Roosevelt sun kamu da cutar COVID-19, adadin da ya wuce kashi 10% na dukkan sojojin kasar Amurka da suka kamu da cutar. Duk da haka, an kori Crozier daga mukaminsa, bisa dalilin wai "ba shi da sanin ya kamata". Sai dai, yadda ake kokarin dora masa laifi ya janyo korafe-korafe daga jama'ar kasar matuka.

A cewar wasu manazartar al'amuran duniya, hakika an sallami kyaftin Crozier bisa wasu dalilai guda 3:

Na farko, yanke masa hukunci kan yadda ya tona asirin kasar. Tun bayan barkewar cutar COVID-19 a kasar Amurka, jama'ar kasar sun dinga nuna rashin gamsuwa kan yadda gwamnati take tafiyar hawainiya wajen daukar matakai. Sa'an nan bayan da aka sanar da wasikar Crozier ga kafofin watsa labaru, dukkan jama'ar kasar sun san gazawar da sojojin kasar suka nuna a fannin tinkarar COVID-19.

Na biyu, yayin da ake fuskantar barkewar annoba a cikin babban jirgin ruwan yakin kasar Amurka, sojojin ruwan kasar na son dora laifi ga kyaftin Brett Crozier, don neman karkatar da hankalin jama'a.

Na uku, a ganin sojojin kasar Amurka, batun nan na bayyana sirrinsu a fili zai raunana karfin sojan kasar, don haka ana son yanke hukunci ga Brett Crozier, don toshe bakin sauran mutane.

Ta wannan batu ma ana iya ganin cewa, yadda ake dora muhimmanci kan moriya maimakon rayukan mutane, ya sa kasar Amurka ta kasa daukar matakai masu dacewa don dakile yaduwar cutar a kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China