Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Najeriya Na Bukatar Yin Hadin Gwiwar Kasar Sin Wajen Dakile Cutar COVID-19
2020-04-04 22:28:39        cri
Hakika annobar da duniya ta samu kanta a ciki sanadiyar cutar novel Corona virus, wato COVID-19 ya yi matukar girgiza duniya kamar yadda aka fara jin labarin cutar a birnin Wuhan na kasar Sin wato China. Kuma hakan ba ya alamta cewa mutanen kasar ne suka kirkiri cutar. Sama da mutane dubu sittin ne suke kamu da cutar kuma har yanzu ana ci gaba da kirga mutanen dake kamuwa da cutar da ta zamo kamar wutar daji. A cikin satittika kalilan da bayyanar cutar ta zamo annoba wa duniya, an rasa iyali da dama, a kulle birane da kasashe ba adadi a fadin duniya. Jama'ar duniya sun shiga halin matsanancin tsoron.

Duk da yake an cika kafar yanar gizo da jita jita da almara da ra'ayoyi mabambamta game da cutar, wasu ma cewa suka yi an kirkiri cutar ne a matsayin wani makamin yaki tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki wa duniya wasu kuwa gani suke yi an kirkiri cutar ce saboda a samu daman sarrafa siyasar duniya. Abun da ya fi dacewa shi ne mu ware wani lokaci.

Na musamman don yin duba na tsanani wa lamarin inda za mu iya fahimtar lamarin ta hanyoyi kamar haka:

•Kasar Sin wato China ita ce kasa ta farko da cutar ta girgiza.

• Wadanda suka rasa rayukansu a kasar sun kai mutum dubu uku da dari uku da talatin da biyar.

•An kulle ko'ina a kasar China har na tsawon watanni biyu.

•Tattalin arzikin kasar China ya shiga halin ni 'yasu.

Amma duk da haka

•Kasar ta China ce ta samar da kashi tamanin cikin dari na bayanan da diniya take bukata game da cutar.

• Sauran kasashen duniya sun shiga rige rigen kirkirar rigakafin cutar ne ta hanyar dogaro da bayanan da masu ilimin kimiyya da fasahar kasar China suka samar game da cutar.

Bugu da kari ya kamata mu tuna cewa:

•Kasashen yammacin duniya su ne suka fi kowa sayan kayayyakin da kasar China ke sarrafawa sa'annan ita ma kasar ta China ta dogara ne da kasashen yammacin duniya wajen shigo da kayayyakin gona cikin kasar ta.

• Kasar ta China har ila yau tana samun kaso mafi yawa na kudin shigan ta ne daga kasuwancin da take yi da kasashen waje.

Tambayar a nan ita ce ta yaya zan durkusar da wanda rayuwa ta kacokam da dogara a kansa?

Ta yaya birnin Wuhan ya magance annobar?

Gwamnatin kasar China a koda yaushe tana bada muhammanci wa al'ummar ta fiye da komai kan haka ne ta yanke muhimman hukunci game da lamarin.

Shin ko kun san yankin Hubei ya samu gudumawa daga dukkan yankunan kasar China da dukkan biranan kasar. Sun samar da duk abubuwan da ake bukata a yankin wajen yakar cutar wanda ya hada da gina katafaren asibitoci cikin kwanaki goma kuma asibiti da zai iya gogayya da dukkan wani asibitin karnin da muke ciki na ashirin da daya.

Ilimin da kasar China ta samu na hana yaduwar cutar Corona virus zai iya zama darasi wa sauran kasashen duniya wajen fuskantar cutar ta COVID-19, kamar yadda wani babban jami'in hukumar lafiya ta duniya ya bayyana wa manema labaru a wata tattaunawa ta musamman da suka yi da shi.

Darussan da ya kamata mu dauka game da cutar.

Yanzu ba lokacin nuna yatsa ba ne, abu mafi a'ala shi ne mu hada karfi da karfe duniya gaba daya ta hade kanta waje guda don kawo karshen wannan annoba ta murar mashako wato Corona virus.

Kamar yadda wata karin magana ta ce, ba'a gane karfin tsintsiya ta hanyar karfin tsinke daya, ana gane karfin tsintsinya ne ta hanyar abun da za ta yi hade waje guda.

Kasar Nigeria tana fama da cutar COVID-19 kuma ya kamata mu fahimci wannan cuta abokiyar gabanmu baki daya. Babu ruwan ta da mai kudi balle talaka, babu yaro balle tsoho. Don haka ya zama dole mu fahimci wannan nauyin ba a kan gwamnati kadai ya dauru ba. Nauyi ne da ya rataya a kan daidaikun mu. Ya zama dole mu zama masu biyayya da matakan da gwamnatoci suke dauka a dukkan matakai, mu kuma kula da tsaftan kai da muhallin mu hadi da ba da kulawa ta musamman wa tsofaffi daga cikin mu wadanda suka fi hatsarin kamuwa da wannan cuta.

Mu tuna cewa duniya ta fuskanci abubuwan da suka fi wannan hatsari don haka wannan ma za mu ga karshen sa.

Allah ya mana Albarka.

Allah ya yi Albarka wa Nigeria.

Allah ya yi Albarka wa duniya baki daya.(Abubakar Shehu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China