Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 2 yayin musayar wuta
2020-04-09 09:39:38        cri

Kimanin mayakan Boko Haram 2 aka kashe, kana wasu da dama suka jikkata yayin musayar wuta da dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, kakakin rundunar sojojin Najeriya ne ya sanar da hakan.

Bernard Onyeuko, mai rikon mukamin kakakin hukumar tsaron Najeriya ya ce, sojojin sun yi nasarar murkushe mayakan 'yan ta'addan a lokacin da suke cikin ayarin wasu motoci 7 da babura masu yawa domin kutsawa wani sansanin sojoji dake yankin Wurge a jihar Borno da yammacin ranar Talata.

A wata sanarwa da Onyeuko ya fitar wacce aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, ya ce, wannan na daga cikin ayyukan da dakarun tsaron Najeriya ke ci gaba da gudanarwa, da nufin kakkabe ayyukan mayakan Boko Haram da ake fama da su a shiyyar arewa maso gabashin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China