![]() |
|
2020-03-31 10:21:16 cri |
Ministan kula da harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya musanta cewa ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19.
Cikin wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya a Lagos, Ministan ya bayyana rahoton na wasu kafafen yada labarai dake zargin ya kamu da cutar a matsayin karya.
Ya ce a matsayinsa na mamban kwamitin ko-ta-kwana kan cutar, wanda shugaban kasar ya nada, an yi masa gwaji tare da sauran mambobin kwamitin a baya-bayan nan, kuma sakamakon ya nuna dukkansu ba su kamu da cutar ba.
Ya ce an san wadanda suka rubuta labarin na da manufar kunyata shi da kuma yada fargaba a lokacin da kasar ke fuskantar annobar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China