2020-04-04 20:20:21 cri |
Rahoto na baya-bayan nan da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ta fitar jiya da daddare, ya nuna cewa, Lagos inda aka fara samun bullar cutar, na da jimilar mutane 109 da suka harbu.
Kawo yanzu, akwai mutane 210 da suka kamu da cutar COVID-19 daga jihohin kasar 14, ciki har da birnin tarayyar Abuja.
Kwamishinan lafiya na jihar Lagos, Akin Abayomi, ya bayyana yayin wani taron manema labarai jiya da dare cewa, hukumomi na bibiyar akalla mutane 2,450 da suka yi hulda da wadanda suka kamu da cutar.
Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba da umarnin takaita zirga-zirga a jihar na tsawon makonni 2, matakin da ya ce an dauka ne bisa shawarar cibiyar NCDC da ma'aikatar lafiya ta kasar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China