Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayan kula da lafiya da Sin ta fitar sun kai na yuan biliyan 10
2020-04-06 15:58:13        cri

Kasar Sin na ci gaba da hadin gwiwa da sauran sassan duniya, a kokarin da ake yi na yakar cutar numfashi ta COVID-19, inda daga ranar 1 ga watan nan na Afirilu zuwa ranar Asabar din karshen makon jiya, kasar ta fitar da kayayyakin kula da lafiya da darajarsu ta kai yuan biliyan 10.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.43.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Lahadi, jami'i a hukumar kwastam ta kasar Jin Hai, ya ce kayayyakin da aka fitar sun hada da takunkumin rufe baki da hanci biliyan 3.86, da rigar kariya ta jami'an lafiya miliyan 37.52, da na'urorin gwajin zafin jiki miliyan 2.41, da kuma na'urar taimakawa numfashi, da tabarau na kare idanu, da kuma kayan gwajin cutar.

A nata tsokacin kuwa, jami'a a ma'aikatar kasuwancin kasar Jiang Fan, cewa ta yi Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen samar da isassun kayayyakin da ake bukata a wannan fanni, muddin dai an bukaci hakan daga gare ta, duba da irin goyon bayan da kasashe da dama suka nuna mata, yayin da take yaki da cutar a cikin gida. Jiang Fan ta ce Sin na dora muhimmancin gaske, ga ingancin kayayyakin kiwon lafiya da take samarwa. A daya bangaren kuma, Sin a shirye take da ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya, ta yadda za a samar da kyakkyawan yanayin samar da kayan kiwon lafiya, da tallafawa yakin da ake yi da cutar COVID-19 a dukkanin sassan duniya. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China