Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin mutane 35 da suka shigo da cutar COVID-19 babban yankin kasar Sin
2020-04-02 16:50:45        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce ta samu rahoton mutane 35 da suka shigo babban yankin kasar da cutar COVID-19 a jiya Laraba, lamarin da ya kawo jimilar wadanda suka shigo da cutar, zuwa 841.

Hukumar ta kara da cewa, akwai kuma wasu 20 da ake zaton sun kamu, wadanda su ma shigo da ita suka yi daga ketare.

Ta ce daga cikin jimilar wadanda suka shigo da cutar, babu wanda ya rasa ransa.

Baya ga haka, daga cikinsu, akwai 140 da aka sallama daga asibitin bayan sun warke, inda 701 ke jinya a asibiti, cikinsu har da guda 18 da yanayinsu ya yi tsanani.

Har ila yau, hukumar ta ce, akwai mutane 153 a babban yankin kasar da ake zaton sun kamu, kuma daga cikinsu, 152 shigo da cutar suka yi daga ketare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China