Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana taimakawa maaikata komawa wajen aikinsu a Hotan na jihar Xinjiang
2020-02-29 17:07:42        cri

An fara amfani da jirgin kasa na musamman wajen kwashe ma'aikata don taimaka musu komawa wajen aikinsu a yankin Hotan na jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda a wannan karo wasu ma'aikata 496 da suka fito daga gundumar Moyu, suka samu damar komawa kamfanoninsu dake sauran wuraren jihar Xinjiang bisa wannan hanya.

Gundumar Moyu wani wuri ne dake fama da talauci. Don neman cimma burin fidda al'ummar gundumar daga kangin talauci a karshen shekarar da muke ciki, ana ta kokarin daidaita ayyukan hana yaduwar cutar COVID-19 gami da taimakawa jama'a samun aikin yi don rage talauci a wurin.

Tun daga farkon bana, hukumar yankin Hotan, ta riga ya kwashe mutane 4018 zuwa wuraren aikinsu, ta hanyoyin jirgin sama, da jirgin kasa, da bas na musamman. Cikin wadannan mutane har da masu fama da talauci 1,549. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China