Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 ya wuce dubu 230 a duniya
2020-03-21 15:11:28        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar da wani sabon rahoto game da yanayin yaduwar cutar COVID-19 a duniya, inda ta ce zuwa kiminin karfe 12 na dare, a ranar 19 ga wata, bisa agogon yankin tsakiyar nahiyar Turai, an samu masu kamuwa da cutar COVID-19 234,073 a duk duniya, ciki har da wasu sabbin mutane 24,247 da suka kamu da cutar, gami da wasu 9,840 da suka mutu sakamakon cutar, cikin har da sabbin wasu 1,061 da suka mutu.

Babban sakataren WHO Tedros Ghebreyesus, ya bayyana a wajen wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland, a jiya cewa, yadda aka daina samun sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a birnin Wuhan na kasar Sin ya karfafa wa mutanen kasashe daban daban gwiwa, da ba su kyakkyawan fatan cewa, duk tsananin da wuyar yanayi, to, akwai damar samun sauki.

Ban da haka kuma, jami'in ya ce, duba da yadda ake fama da matsalar karancin kayayyakin kariya a kasashe daban daban, hukumar WHO za ta samar da tallafi. Yanzu haka hukumar ta tabbatar da cewa, wasu kamfanonin kasar Sin sun riga sun yarda da samar da kayayyakin da ta ke bukata, inda a halin yanzu ake kokarin tabbatar da matakan da za a bi don gudanar da wannan aiki. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China