Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CGTN ya bankado karyar da CNN ta yi kan zargin rushe kaburburan 'yan kabilar Uygur a Xinjiang
2020-01-14 13:22:41        cri

Kwanan baya, kafar yada labarai ta Amurka CNN ta ba da labarin cewa, marubucin wakokin 'dan kabilar Uygur wanda ke rayuwa a birnin London na Birtaniya Aziz Isa Elkun, ya ce, bai gane kabarin mahaifinsa ba, saboda wai gwamnatin jihar Xinjiang ta rushe kaburburan 'yan kaiblar Uygur a jihar, kuma ya jaddada cewa, wannan wani mataki ne da gwamnatin Sin ta ke dauka don goge al'adun Uygur baki daya. Amma, a gidansa dake gundumar Xayar na yankin Aksu na jihar, mahaifiyar Aziz, Hepizem Nizamidin ta jagoranci 'yan jaridar CGTN, gidan telibijin kasa da kasa na kasar Sin zuwa kabarin mahaifin Aziz, inda ta ba da wani labari na daban.

Hepizem Nizamidin ta ce, musulmai na kabilar Uygur dake zaune a yankunan karkara kullum su kan binne iyalansu da suka rasu a cikin kasa, mahaifin Aziz shi ma haka. Amma a wasu lokutan kaburburan su kan lalace, saboda iska da ruwan sama da kare da kyanwan daji, hakan ya sa kauyawan wurin su kan gyara wadannan kaburbura, kuma sun kai korafi ga hukumar kula da harkokin cikin gida ta jihar. Saboda haka, gwamnatin jihar ta kwashe shekaru fiye da 10 tana jin ra'ayoyin jama'ar wurin tun daga shekarar 2000, don gina wata sabuwar makabarta ta zamani. Hepizem Nizamidin ta kaura kabarin mahaifin Aziz zuwa wannan wuri a karshen shekarar 2018.

Hepizem Nizamidin ta gayyawa 'yan jaridar CGTN cewa, sun kaurar da kabarin bisa burin kansu, sabuwar makabartan tana da inganci sosai, kuma iska da ruwan sama ba za su iya lalata ta ba, an kuma kewaye ta da itatuwa da furanni, akwai kyan gani a lokacin zafi, mun gamsu matuka. Ta kara da cewa, yanzu mijinta yana kwance a wannan wuri mai kyau, za ta rika ziyartar mijinta a duk lokacin da ta yi begen sa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China