Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin AfDB ya samar da lamunin dala biliyan 3 domin tunkarar tasirin COVID-19 a Afrika
2020-04-01 11:05:16        cri
Bankin raya nahiyar Afrika AfDB, ya ce ya samar da jimilar dala biliyan 3 ta hanyar takardun lamuni mai zangon shekaru 3, domin taimakawa tunkarar tasirin cutar COVID-19 kan tattalin arziki da zaman takewa a nahiyar.

Wata sanarwa da bankin ya fitar, ta ce wannan wani bangare ne na matakan tunkarar mummunan tasirin annobar akan kasashe da bangarori masu zaman kansu na nahiyar.

Sanarwar ta ce fitar da lamunin na dala biliyan 3, wani bangare ne na farko cikin matakan tunkarar annobar da bankin zai sanar a nan gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China