Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka rasu sakamakon COVID-19 a Afirka ya kai mutum 64 bayan bullar cutar a kasashen nahiyar 43
2020-03-25 20:39:34        cri
Ya zuwa Larabar nan, yawan wadanda suka rasu sakamakon kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Afirka sun kai mutum 64, cikin mutane sama da 2,412 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasashen nahiyar 43.

A cewar cibiyar yaki da cututtuka da kandagarkin yaduwarsu ta nahiyar, ko Africa CDC a takaice, kasashen da ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar sun hada da Afirka ta kudu mai mutane 709, sai Masar mai mutum 402, da Algeria mai mutane 264, da Morocco mai mutum 170.

Cibiyar ta Africa CDC ta kuma bayyana cewa, akwai mutane 203 da suka warke bayan kamuwa da cutar ta COVID-19, a kasashen nahiyar 14. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China