Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika 24 sun rufe iyakokinsu yayin da ake fama da annobar COVID-19
2020-03-28 16:41:26        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika (CDC), ta bayyana a jiya cewa, kimanin kasashen nahiyar 24 sun rufe iyakokinsu saboda fargabar yaduwar cutar COVID-19.

Cibiyar wadda ke karkashin Tarayyar Afrika AU, mai kasashe mambobi 55, ta kuma jadadda cewa akwai wasu kasashe 7 da suka haramta tafiye tafiye zuwa wasu kasashe, yayin da wasu 7 suka haramta shiga kasashensu daga wasu kasashen.

Cibiyar ta kara da cewa, wasu daga cikin kasashen na barin zirga-zirgar jiragen dakon kaya da na bukatun gaggawa.

Har ila yau, cibiyar ta bayyana cewa, adadin wadanda suka mutu a nahiyar sanadiyar cutar COVID-19 ya kai 83, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu ya haura 3,243, ya zuwa jiya Juma'a.

A cewarta, ya zuwa safiyar ranar Alhamis, kasashen da cutar ta fi Kamari a nahiyar sun hada da Afrika ta Kudu dake da mutane 927 da suka harbu, sai Masar dake bi mata baya da mutane 495, sai Algeria mai mutane 302 da kuma Morocco dake da mutane 275 da suka harbu.

Bugu da kari, cibiyar ta ce akwai kuma wasu mutane 254 da suka warke daga cutar a fadin nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China