Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na taimakawa wajen samar da kayayyakin yaki da COVID 19 ga kasa da kasa 
2020-03-25 14:07:35        cri

Cutar COVID 19 na yaduwa a duk fadin duniya, a halin da wannan kalubale ya daibaibaye kasa da kasa, Sin na tallafawa kasashen duniya ba tare da bata lokaci ba bisa tunanin raya kaykkaywar makomar Bil Adam ta bai daya.

Da safiyar jiya Talata agogon Hungary, kayayyakin kandagarkin cutar da kasar ta saya daga kasar Sin, suka isa filin saukar jiragen sama na Budapest fadar mulkin kasar, inda firaministan kasar Viktor Orbán ya tarbi ma'aikatan jirgin a filin saukar jiragen sama na birnin.

A wannan rana kuma, shugaban tawagar jakadun Sin dake AU, Liu Yuxi, ya gana da Jami'a mai kula da harkokin jama'a na AU, Amira El Fadil, inda suka rattaba hannu kan wata takardar shaidar karbar na'urar gwada kwayar cutar, wanda shi ne karo na biyu da Sin ta tallafawa nahiyar Afrika.

Amira El Fadil, ta gode da tallafin kayayyakin jiyya da gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na Sin suka baiwa nahiyar. Ta ce, Sin sahihiyar aboki ce kuma 'yar uwar Afrika. Ta ce nahiyar na fatan kara hadin kai da kasar Sin ta fuskar yakar cutar da koyon da fasaha da dabara masu inganci daga wajenta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China