Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rwanda ta rufe gidajen adana dabbobi biyo bayan barkewar cutar COVID-19
2020-03-21 16:38:01        cri
Kasar Rwanda ta sanar da dakatar da yawon bude ido da ayyukan bincike a wasu gidajen adana dabbobi 3 daga jiya Juma'a.

Hukumar kula da raya kasar ta bayyana cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya cewa, an dakatar da yawon bude ido da ayyukan bincike, a wani mataki na wucin gadi, a wuraren adadna dabbobi 3 da suka hada da Volcanoes da Mukura-Gishwati da Nyungwe, saboda annobar cutar COVID-19.

A cewar sanarwar, yayin da har yanzu ba a kai ga gano ko dabbobin dawa na iya kamuwa da cutar ba, akwai wasu nau'ikan birrai dake iya kamuwa da cututukan numfashi irin na dan Adam.

Hukumar ta kara da cewa, wurin adana dabbobi na 4 mai suna Akagera National Park, zai ci gaba da karbar baki, inda aka dauki matakan sa ido kan cutar.

A farkon watan nan ne, hukumar ta yi bitar ka'idojin izinin yawon bude ido, da nufin ba masu shirin ziyartar kasar domin yawon bude ido damar sauya lokacin ziyara, tare da dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, yayin da ake tsaka da fama da bazuwar cutar COVID-19.

A jiya Juma'a, kasar ta bada rahoton samun sabbin mutane 6 da suka kamu da cutar, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar zuwa 17, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China