Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rwanda ta yabawa kasar Sin bisa yadda take tunkarar cutar Corona
2020-02-01 16:07:36        cri
Ministan kula da harkokin wajen Rwanda Vincent Biruta, ya gana da Rao Hongwei, Jakadan Sin a kasar, a jiya Juma'a, inda ya bayyana goyon bayan kasarsa ga gwamnati da al'ummar Sin wajen yaki da barkewar cutar numfashi ta Corona.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Rwanda ta fitar jiya, ta yabawa yadda kasar Sin ke tunkarar cutar numfashi ta Corona da kuma yadda take taimakawa bakin dake kasar, ciki har da 'yan Rwanda.

Sanarwar ta ruwaito Ministan na cewa, Rwanda na bayyana godiya ga kasar Sin game da yadda take tafiyar da ayyaukan yaki da cutar Corona da kuma yadda take taimakawa bakin dake lardin Hubei, ciki har da 'yan Rwanda. Yana mai cewa, suna da tabbacin kasar Sin za ta iya shawo kan cutar tare da taimakawa kasashen waje kan matakan dakileta.

Har ila yau, Ministan ya kuma godewa Jakadan bisa taimakon kayayyakin abinci da sauran abubuwan bukata da hukumomin lardin Hubei suka ba 'yan Rwanda 155 dake zaune a lardin, bisa hadin gwiwar ofishin jakadancin kasar dake birnin Beijing. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China