Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rwanda tana maraba da hukunta madugun kisan kare dangin kasar da kotun Belgium
2019-12-21 16:53:21        cri
Hukumar dake yaki da kisan kiyashi ta kasar Rwanda (CNLG), ta ce matakin da babbar kotun Brussels ta dauka a ranar Alhamis na hukunta madugun kisan kare dangi da aikatan laifukan yaki na kasar, wata babbar nasara ce.

Fabien Neretse, mai shekaru 71, a ranar Juma'a an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 25, a yayin zaman kotun ta kasar Belgium na ranar Alhamis.

Ana tuhumar madugun da laifukan kisan kare dangi da aikata laifukan yaki kan tsiraru 'yan kabilar Tutsi a lokacin fadan da ya barke a kasar Rwanda na tsawon watanni uku a shekarar 1994, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da miliyan 1.

A cewar sanarwar da hukumar CNLG ta fitar, Neretse, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa a lokacin gudanar da shara'ar, shi ne mutum na farko da aka yankewa hukunci a kasar Belgium game da laifukan kisan kare dangi.

Kotun majistiri ta kasar Belgium ta tanadi hujjoji a cikin shekaru masu yawa kan batun, tun daga lokacin da aka tsare Neretse a kasar Faransa a shekarar 2011. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China