Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rwanda ta rufe makarantu da jami'o'i da wuraren ibadu saboda cutar COVID-19
2020-03-15 16:26:28        cri
Ma'aikatar lafiyar kasar Rwanda ta sanar a jiya Asabar cewa gwamnatin kasar ta rufe dukkan makarantu, jami'o'i da wuraren ibadu a duk fadin kasar har tsawon makonni biyu domin dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Sanarwar ta ce matakin rufe wuraren ibadun kasar zai fara ne tun daga yau Lahadi, inda aka bada umarnin yin ibadu daga cikin gidaje, yayin da makarantun kasar da manyan cibiyoyin ilmin kasar za su ci gaba da zama a rufe daga ranar Litinin mai zuwa.

A cewar sanarwar sabbin matakan da aka dauka za su taimakawa kasar wajen takaita barazanar yaduwar cutar COVID-19 a kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China