Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karairayin Mike Pompeo da Amurka mai kauce hanya
2020-02-27 21:54:18        cri

A ganin jama'ar Amurka, kowane dan siyasa na da alamarsa. A matsayin tsohon sakataren harkokin waje, Henry Kissinger na wakiltar mai wayin kai a fannin diplomasiyya, amma abin da Mike Pompeo zai baiwa jikokinsa babu komai a ciki sai karya.

Jaridar "The Guardian" ta Birtaniya ta wallafa wani sharhi kwanan baya, inda ta yi zambo kan Mike Pompeo cewa, in dai ba Pompeo na son zama san-kiran Birtaniya ba ne, bai kamata ya furta wadannan kalmomi marasa ma'ana a gun taron tsaro da aka yi kwanan baya a Munich ba, inda ya ce, "kawancen kasashen Turai da Amurka bai samu koma baya ba ko kadan, kasashen yamma na samun nasara, muna samun nasara."

Wannan sharhi ya kuma nuna cewa, Amurka da Birtaniya ba su cimma nasara tare ba, a maimakon haka, suna da bambancin ra'ayi sosai. Alal misali, a kan batun fasahar 5G na kamfanin Huawei, dangantakar dake wadannan kawaye biyu ta tsage. Sharhin ya kuma nuna cewa, an soki ganawar shugabannin kasashen biyu da aka shirya yi a farkon watan Maris a birnin Washington.

Birtaniya ta riga ta yarda da kamfanin Huawei, ya shiga aikin kafa fasaha 5G a kasar, abin da ya shaida cewa, kimiya da kuma fasahar Huawei na da inganci kwarai, kuma ya alamta cewa, bayan Birtaniya ta janye jikinta daga EU, tana ci gaba da burinta na hadin kanta da Huawei. Amma, a nata bangare, Amurka tana yunkurin kawo cikas ga bunkasuwar sana'ar kimiya da fasaha ta kasar Sin, har ma tana yunkurin tilastawa sauran kasashe da su bi hanya irin ta ta.

Daga matsayin da aka dauka kan fasahar 5G na Huawei zuwa ga yarjejeniyar cinikayyar Amurka da Birtaniya nan gaba, sharhin ya bayyana matsayin da Amurka ke dauka, na nuna fin karfi da babakere a duniya, da cin zarafin saura, da kuma yaudara da matsin lambar da Amurka ke yi a cikin yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen biyu, duk abubuwan dake kasancewa babban kalubale ne ga Birtaniya.

Amurka ta yi watsi da kawayenta, ba ma kawai a Turai ba, karkashin tunaninta na mayar da wani bangare saniyar ware. Gwamnatin Amurka a wannan karo na ganin cewa, kowa na cin zarafin Amurka, saboda haka, ministoci masu mukami yanzu, suna yunkurin aiwatar da manufofin cin zalin wasu marasa karfi, da nufin kafa wani sabon tsari na siyasa da tattalin arzikin duniya bisa ra'ayin kare kai.

Mike Pompeo na ba da babbar gudunmawa, wajen tsayarwa, ko aiwatar da wadannan manufofi ko tsare-tsare marasa kyau. A kan matsayin sakataren harkokin wajen Amurka, ba ya son samun ci gaban diflomasiyya ba, a maimakon haka yana yunkurin aiwatar da ra'ayin yakin cacar baki, har ya baza jita-jita, da yin surutu a kafofin yada labarai ba tare da gajiya ba.

A lokacin da ake fuskantar mumunan tasirin cutar ta COVID 19 a duniya, Pompeo ya ba da kariya ga bayanan da jaridar "The Wall Street" ta wallafa, masu cike da ra'ayin nuna bambancin kabila, har ma ya wulakanta sunan kasar Sin a duniya, saboda ganin Sin ta dauki matakin da ya dace don mai da martani ga jaridar.

Amma kafin nan, Pompeo ya taba bayyana gaskiya a kalamansa, inda ya ce "Mun yi karya, mun baza jita-jita, har ma mun yi sata." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China