Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta zurfafa gyare-gyare a ayyukan gwamnati da karfafa samar da aikin yi
2020-03-18 11:59:42        cri

Kasar Sin za ta zurfafa gyare-gyare a ayyukan gwamnati da samar da sabbin dabarun ingiza ci gaba da sabbin nau'ikan sana'o'i ta intanet da kuma karfafa samar da aikin yi.

Taron majalisar gudanarwar kasar da ya gudana jiya Talata, karkashin jagorancin Firaminista Li Keqiang ne ya bayyana haka, inda Firaministan ya ce wajibi ne a zurfafa gyare-gyare a ayyukan gwamnati da samar da karin dabaru a fannin intanet, yana mai cewa dole ne a inganta kananan kasuwanci da kirkire-kirkire a fadin kasar, domin samar da karin damarmakin fara sabbin kasuwanci da samar da aikin yi.

Ya ce karfafa samar da aikin yi shi ne abun da suka sanya a gaba a bana. Kuma kananan kamfanoni na da muhimmanci wajen samar da aikin yi. Don haka, dole ne sassan gwamnati masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen taimakawa irin wadannan kamfanoni.

Yayin taron, an kuma bukaci a dage duk wata ka'ida da ba ta dace ba dake tarnaki ga komawa bakin aiki domin ba karin mutane damar komawa aiki da samun kudin shiga nan bada dadewa ba, la'akari da yadda yanayin annobar ke kara sauki.

Li Keqiang ya ce dole ne a gaggauta samarwa tare da gabatar da dabarun da za su taimakawa sabbin kasuwanci da kirkire kirkire, da bunkasa samar da ayyukan yi ga wadanda suka kammala jami'a da 'yan cin rani daga kauyuka da sauran muhimman rukunonin jama'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China