Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan shagunan Starbucks za su kai 6,000 a Sin nan da shekarar 2022
2020-03-16 10:35:06        cri
Kamfanin sayar da Gahawa da kayan ciye ciye na Starbucks na kasar Amurka, ya ayyana shirin sa na kara yawan shugunan sa a kasar Sin zuwa 6000 nan da shekarar 2022, matakin da zai shigar da jari da yawan sa zai kai dala miliyan 130.

Cikin wata takardar sanarwa, kamfanin ya ce zai samar da shaguna na zamani a shekarar 2022, karkashin shirin samar da salon zamani na shaguna da kamfanin ya yiwa lakabi da CIP, wanda ke nuni ga burin kamfanin na karade sassan duniya da hajojin sa na abinci, inda zai karfafa kasuwannin sa na Amurka da Sin.

A matsayin shirin CIP na Starbucks, na harkar dake kunshe da jari mafi yawa da kamfanin zai zuba a wajen Amurka, kuma irin sa na farko a Asiya, shirin zai kunshi samar da wuraren sarrafa Gahawa, da wuraren ajiya da rarraba kaya, da samar da ayyukan yi, da damammakin samar da kwarewa don bunkasa kasuwar Gahawa a Sin, wanda hakan zai karfafa ginshikin ci gaban kasuwancin kamfanin a kasar Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China