Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daukacin manyan masanaantun kasar Sin sun kusa komawa bakin aiki
2020-03-18 11:55:29        cri

Mai magana da yawun hukumar tsara ayyukan samar da ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin Meng Wei, ta ce daukacin manyan masana'antun kasar Sin sun kusa komawa bakin aiki.

Meng Wei ta ce kaso 90 bisa dari na manyan masana'antun kasar dake a matsayi na larduna, ban da Hubei inda cutar ta fi kamari, sun koma bakin aiki bayan fama da cutar numfashi ta COVID-19, wanda hakan sakamako ne na matakan farfado da ayyuka da yankunan kasar daban daban suke aiwatarwa.

Jami'ar ta ce kusan kaso 100 bisa 100 na masana'antun dake lardin Zhejiang, da Jiangsu, da Shanghai, da Shandong, da Guangxi, da Chongqing sun kammala komawa bakin aiki.

Alkaluman amfani da lantarki a yankunan, sun nuna yadda muhimman sassan sarrafa hajojin masana'antu ke farfadowa. Kaza lika kamfanonin sarrafa karafa sun koma aiki gadan gadan kamar yadda suke yi a shekarar bara, yayin da kamfanonin harhada magunguna, da na hada sinadarai, da kamfanonin laturoni, suka fara amfani da lantarkin da ya kai kaso 90 bisa dari, na yawan lantarkin da suke amfani da shi kafin aukuwar wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China