Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudin da kamfanonin gwamnatin Sin ke samarwa domin yaki da talauci zai kai yuan biliyan 3.357 a bana
2020-03-14 17:10:39        cri
Hukumar kula da kadarorin kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana cewa, a bana, manyan kamfanoni mallakar gwamnatin kasar, za su kebe jarin da yawansa zai kai kudin Sin yuan biliyan 3 da miliyan 357 domin tallafawa yankunan dake fama da talauci.

Tun daga shekarar 2015, manyan kamfanonin sun samar da kudin yuan biliyan 20 da miliyan 600 ga yankunan dake fama da talauci a fadin kasar, inda kawo yanzu gundumomi 219 dake cikin 246 dake samun tallafin kamfanonin, suka kubutar da kansu daga talauci.

Kana asusun zuba jari kan sana'o'in yankunan dake fama da talauci na manyan kamfanonin gwamnatin kasar da hukumar kula da kadarorin kasa ta majalisar gudanarwar kasar ta kafa, ya mallaki kudin yuan biliyan 31, kuma kawo yanzu ya zuba jarin da yawansa ya kai yuan biliyan 22, tare kuma da tattara kudin yuan biliyan 210 daga bangarori daban daban. Har ila yau, ya kuma samar da guraben aikin yi ga mutane dubu 420 a yankunan dake fama da fatara, inda a ko wace shekara yake samar musu kudin shiga yuan biliyan 3 da miliyan 500.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China