Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da rahoton keta hakkin dan Adam na Amurka na 2019
2020-03-14 17:16:55        cri

 

Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da rahoto kan keta hakkin dan Adam na kasar Amurka na shekarar 2019 a jiya Juma'a, inda aka tono hakikanin yanayin da kasar ke ciki a bangaren keta hakkin dan Adam daga fannoni bakwai.

A cikin rahoton, an yi nuni da cewa, Amurka tana nuna fin karfi a fadin duniya. A ko wace shekara, ta kan fitar da rahoton keta hakkin dan Adam na wasu kasashen duniya, inda take zargin wasu kasashe ko yankuna wadanda ba su dauki matakan da suka dace da moriyarta ba, kana ta yi watsi da yanayin da ita kanta ke ciki wajen keta hakkin dan Adam.

Rahoton ya ce hakika, Amurkawa ba su da 'yancin 'yan asalin kasa ko 'yancin siyasa, inda zaben kasar ya kasance wani salon barnar kudi. Alal misali, daukacin 'yan takarar shugabancin kasar sun riga sun tattara kudin da ya kai dala biliyan 1 da miliyan 80 domin gudanar da babban zaben bana, kuma kawo yanzu sun riga sun kashe dala miliyan 531 daga ciki.

Ya kara da cewa, Amurka kasa ce mafi tsananin fama da karfin bindiga, inda jimilar laifuffukan da aka aikata a kasar ta hanyar bude wuta a shekarar 2019 da ta gabata, ta kai 415, wadanda suka yi sanadin rayukan mutane 39,052.

Rahoton na ganin cewa, Amurka ita ce kasa mafi son tayar da yaki a tarihi, kuma ta kan fice daga yarjejeniyoyin da ta daddale, ko kakkabawa wasu kasashe takunkumi ko kai wa wasu hari kamar yadda take so. Ya ce tun daga shekarar 2001, Amurka ta yi ta kai hari kan wasu kasashe, inda adadin kudin da ta ware a bangaren ya kai sama da dala biliyan 6400, kana adadin mutanen da suka rasu a cikin yake-yaken ya kai fiye da dubu 800. Wurare da dama a fadin duniya sun shiga cikin tashin hankali, inda mazauna wuraren ke fama da mawuyacin yanayin jin kai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China