Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samar da dabarun yaki da cutar COVID-19 ga kasashen duniya
2020-03-14 17:15:16        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping,ya tattauna da babban sakataren MDD Antonio Geterres ta wayar tarho a ranar Alhamis, inda ya gabatar da dabarun kasar Sin na yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Xi Jinping, ya ce, ya dace yanzu kasashen duniya su hada kai domin daukar matakai ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a dakile annobar bada jimawa ba.

Ya ce bayan kokarin da daukacin al'ummun kasar Sin suka yi, an samu sakamako a bayyane wajen hana yaduwar annobar, kuma kamfanonin dake kasar suna dawowa bakin aiki cikin lumana, sai dai, annobar tana bazuwa a sauran kasashe cikin sauri, inda aka shiga wani mataki na daban na yaki da ita.

Dangane da yadda za a yaki cutar a fadin duniya yanzu, Bruce Aylward, babban mashawarcin shugaban hukumar lafiya ta duniya na ganin cewa, fasaha mafi muhimmanci da kasar Sin ta samu ita ce sauri, wato matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka cikin sauri sun samar da dama da kuma lokaci ga sauran kasashe yayin da suke kokarin hana bazuwar kwayoyin cutar.

Amma abun takaici shi ne, wasu kasashe ba su yi amfani da damar ba. Hukumar lafiya ta duniya ita ma ta bayyana damuwa kan wasu kasashe da ba su mai da hankali kan batun ba, inda suka gaza daukar matakai a kan lokaci, har ta yi kashedin cewa, lokaci da damar da kasar Sin ta samar suna raguwa

Abun farin ciki shi ne, a jiya Jumma'a da safe, aka kafa tsarin hada gwiwa na aikin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 tsakanin kasar Sin da Koriya ta Kudu, kuma sassan biyu sun kira taro karo na farko ta bidiyo. Wannan lamarin zai taimakawa Sin da Koriya ta Kudu wajen dakile annobar, har ma da sauran kasashen duniya baki daya.

Yanzu cudanyar tattalin arzikin duniya tana kara habaka. A nan gaba, akwai yiwuwar sake aukuwar wani abu ba zato ba tsammani, kamar annobar da ake fuskanta yanzu, idan har ana son shawo kan kalubalen dake gaban dan Adam, hanya daya kacal da ake da ita, ita ce hadin kan kasa da kasa, kamar dai yadda shugaba Xi Jinping ya jaddada.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China