Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taimakawa wasu, taimakon kai ne a lokacin da ake tunkarar kalubale
2020-02-26 22:15:28        cri

A yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Talata a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ambato wani karin maganar Sinawa da ke da ma'anar "Yaba kyauta tukuici", wanda kuma ke nuni ga nagartar Sinawa. A nan jimlar Mr. Zhao na nuni ga godiyar da kasar Sin ke yi ga taimako da al'ummar kasa da kasa suka ba ta, da kuma niyyar kasar Sin, na sauke nauyin dake wuyanta, na kiyaye tsaron duniya gaba daya.

An lura cewa, bayan barkewar cutar COVID 19, shugabannin kasashe 170, da kungiyoyi 40, sun aiko wasiku, ko buga waya ga kasar Sin, don nuna mata goyon baya, har ma wasu al'umommin kasashe daban-daban sun samar da tallafin kayayyaki kyauta, don karawa kasar Sin kwarin gwiwa ta hanyoyi daban-daban. Daga cikin wadannan kasashe, akwai kasashe masu wadata, da kuma kasashe masu tasowa.

Alal misali, gwamnatin Ghana ta baiwa birnin Wuhan abubuwan rufe baki da hanci samfuri N95 dubu 100 cikin gaggawa. Kasar Equatorial Guinea kuwa ta ba da kudi kyauta har dala miliyan 2 da dai sauransu. Duk da cewa, kasashen Afrika ba su da wadata sosai, amma duk da haka sun ba da matukar taimakonsu gwargwadon karfinsu.

Al'ummar Sinawa ba za su manta da taimakon da aka ba ta ba, kuma duk wanda ya yi mata alheri za ta saka masa.

Ya zuwa yanzu dai, ofishin jakadancin Sin dake Iran, da kuma kamfanonin jarin Sin dake Iran, sun samarwa kasar Iran abubuwan rufe baki da hanci dubu 250. Ban da wannan kuma, saboda ganin Japan na da karancin kayayyakin gwajin cutar, Sin ta mika mata wasu nau'urorin gwajin cutar. Ga kasashen Afrika kuwa, Sin na kokarin ba da taimako gare su bisa halin da suke ciki.

Shugaban hukumar zartaswar AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana a kwanan baya cewa, tun barkewar cutar, cibiyar dakile cuta ta nahiyar Afrika, ta gudanar da aikin kandagarki, da yaki da yaduwar ta a nahiyar, ba tare da bata lokaci ba, bisa taimakon da WHO da kuma cibiyar dakile cuta ta kasar Sin suka samar musu. A cikin makonni 3 kacal, yawan kasashen dake iya binciken cutar ya karu zuwa 26 daga 2 a nahiyar, kuma an yi shirin kara wannan adadi zuwa 47 a karshen watan Fabrairu da muke ciki.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bugawa firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali wayar tarho a ran 25 ga wata, inda ya bayyana cewa, Sin na fatan kara baiwa kasashen Afrika karin taimako, ciki hadda na'urorin gwajin kwayoyin cutar da dai sauran kayayyakin jinyya, wadanda ake matukar bukata. Matakin da ya bayyana cewa, Sin da Afrika na marawa juna baya, da taimakawa juna a cikin mawuyancin hali.

A halin yanzu dai, Sin na kokarin shiga aikin yaki da kandagarkin cutar, da baiwa sauran kasashe taimako, amma a maimakon haka, wasu 'yan siyasa da kafofin yada labarai na Amurka, na yunkurin baza jita-jita kan kasar Sin ba tare da mai da hankali kan sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa sauran kasashen a kan lokaci ba.

A lokacin da ake fuskantar kalubale, taimakon wasu taimakon kai ne.

Taimakawa juna, da goyon bayan juna, hanya ce daya tilo da za a bi wajen tinkarar wannan mumunar cuta, da dawo da yanayin doka da oda a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China