Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Bai dace Amurka ta zargi kokarin Sin na dakile cutar COVID-19 ba
2020-03-12 19:53:04        cri
A yau Alhamis ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya soki wasu jami'an kasar Amurka, saboda zargi kokarin da kasar Sin take yi na dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda ya bayyana cewa, ba da dadewa ba, hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa, annobar ta kasance ta duniya baki daya, lamarin da ya nuna cewa, annobar ta riga ta kasance kalubalen dake gaban daukacin bil Adama, a don haka yana fatan wasu jami'an Amurka, za su mai da hankali kan aikin dakile ta, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, a maimakon zargin kokarin kasar Sin. Ya ce hakika zarginsu ba shi da tushe, ba zai kuma taimakawa aikin dakile annobar a cikin kasar ta Amurka ba.

Geng ya yi nuni da cewa, ya dace kasa da kasa, su hada kai su yi kokari tare, ta yadda za su cimma burin ganin bayan annobar ba da jimawa ba, kuma zargi maras tushe ba shi da wani amfani ko kadan, ana kuma fatan wasu jami'an Amurkan, za su yi biyayya ga hakikanin abubuwa, su kara mai da hankali kan aikin dakile annobar. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China