Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta yi aiki tare da sauran kasashe wajen kawo karshen COVID-19 a matakin kasa da kasa
2020-03-12 19:51:43        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce yakin da kasar Sin ke yi da cutar numfashi ta COVID-19, muhimmin aiki ne na yakar cutar a matakin kasa da kasa.

Geng na wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Alhamis, inda ya ce a mataki na gaba, Sin a shirya take ta ci gaba da aiwatar da managartan matakai, na kandagarki da shawo kan cutar a cikin gida, yayin da take tallafawa aikin yaki da cutar a matakin kasa da kasa.

Jami'in ya kara da cewa, bayan barkewar cutar COVID 19, gwamnatin Sin ta dauki ingantattun matakai, da tsauraran manufofin kandagarki da shawo kan cutar, ta kuma kaddamar da yaki na gaba da gaba da annobar. Ya ce bayan aiki tukuru, matakan da aka dauka a kasar sun haifar da kyakkyawan sakamako a matakai daban daban. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China