Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kan bakan ta na cimma kudurin kawar da talauci
2020-03-12 21:00:36        cri
Daraktan ofishin dake kula da ayyukan rage talauci da samar da ci gaba, na majalissar gudanarwar kasar Sin Liu Yongfu, ya ce Sin na kan bakan ta na cimma burin kakkabe talauci tsakanin al'ummun ta, duk kuwa da tasirin cutar numfashi ta COVID-19 da kasar ke fama da ita.

Liu Yongfu, ya ce ya zuwa makon jiya, kusan ma'aikata 'yan ci rani miliyan 3, daga yankuna masu fama da matsanancin talauci, sun koma bakin ayyukan su. Ya kara da cewa, ya zuwa 6 ga watan nan na Maris, an ci gaba da aiwatar da daya bisa 3 na ayyukan yaki da fatara da aka tsara, ana kuma gaggauta ci gaba da dawowar saura.

Jami'in ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, an kusa kammala ayyukan yaki da talauci da aka tsara aiwatarwa a kasar baki daya, yayin da ya zuwa karshen shekarar 2019, adadin mutane da ba sa samun isasshen abinci ya yi kasa zuwa miliyan 5.51, sabanin mutum miliyan 98.99 da ake da shi a kasar a shekarar 2012. Kaza lika a bana, adadin gundumomin kasar dake cikin matsanancin talauci ya ragu zuwa 52.

A daya bangaren kuma, nan gaba kadan, za a fitar da ka'idojin lura da ayyukan yaki da fatara, wadanda za su hana al'ummar da suka samu fita daga kangin talauci sake komawa. Har ila yau, za a aiwatar da matakan tabbatar da samar da ilimi na wajibi, da bunkasa sana'o'i, da ilimin gaba da firamare, da na kananan yara a yankunan dake fama da fatara, a wani mataki na dakile yaduwar talauci tun daga tushe.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China