Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sallami mutane 1,578 daga asibiti a babban yankin Sin da suka warke daga COVID-19
2020-03-11 13:10:04        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, an sallami jimillar marasa lafiya 1,578 daga asibiti a babban yankin kasar Sin, bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar numfashi ta COVID-19.

Hukumar ta bayyana a rahoton rana-rana da take fitarwa game da yanayin cutar ta COVID-19 cewa, ya zuwa jiya Talata, baki daya an sallami marasa lafiya 61,475 daga asibiti, bayan sun warke daga wannan cuta. Ya zuwa jiya Talata, an ba da rahoton jimillar mutane 80,778 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin, kana mutane 3,158 sun mutu sanadiyar cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China