Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kokarin dakile cutar COVID-19 a fadin duniya
2020-03-12 19:48:30        cri
Kwanan baya ministan harkokin wajen kasar Italiya Luigi Di Maio, ya buga waya ga takwaransa na kasar Sin Wang Yi, inda ya bayyana cewa, "Italiya tana fama da karancin kayayyaki da kuma na'urorin likitanci, tana fatan kasar Sin za ta samar mata da tallafi cikin gaggawa."

Italiya dai kasa ce da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta yi kamari cikin ta a Turai, inda ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya, yawan 'yan kasar da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 12,462, ciki hadda 827 da suka rasu.

A daidai wannan mawuyacin hali, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta samar da kayayyaki da na'urorin likitanci, kamar kayan rufe baki da hanci ga kasar ta Italiya, inda tun a jiya, ta tura wata tawagar kwararrun likitoci 7 masu aikin sa kai daga kungiyar Red Cross ta kasar Sin zuwa ga kasar, tare da kayayyakin likitanci da dama, domin taimakawa kasar wajen dakile annobar.

Ba ma kawai kasar Sin tana taimakawa Italiya ba ne, ta ma riga ta yi kokari matuka a cikin wata guda da wani abu, da ya gabata, inda kawo yanzu ta samu sakamako bisa mataki na farko. A sa'i daya kuma, ta samar da damar dakile annobar ga sauran kasashe, kana kasar Sin ta yi musanyar bayanan kwayar cutar a fili tare da hukumar lafiya ta duniya, har ta sanar da rahoton sabbin mutanen da suka kamu da cutar a kan lokaci, ga kasashe da yankunan da abin ya shafa.

Dalilin da ya sa kasar Sin ta yi haka shi ne, domin nuna godiya ga kasa da kasa, bisa goyon bayan da suka nuna mata, yayin da take kokarin dakile annobar, tana sauke nauyin tsaron lafiyar jama'a a fadin duniya, kana tana son aiwatar da manufar samar da kyakkyawar makomar bil Adama, wadda shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar.

Amma wasu kasashe sun yi watsi da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, har ta kai sun kawo illa ga aikin dakile annobar. Alal misali kasar Amurka, wadda kasa ce mafi ci gaba a duniya, tana bata lokaci wajen shawo kan annobar, har ma ta sanar da cewa, za ta rage kudin da take bayarwa domin goyon bayan hukumar lafiya ta duniya, kana ba ta cika alkawarin samar da tallafi ga sauran kasashe da ta yi ba, kuma ba ta soke takunkumin da ta kakkabawa kasar Iran ba. Duk wadannan sun nuna son kai na Amurka, wato har kullum tana mayar da moriyar kanta da farko.

Wannan annoba dai tana shafar daukacin bil Adama, don haka ya dace kasa da kasa su hada kai, kuma hakikanin aikin dakile annobar da kasar Sin take gudanarwa ya shaida cewa, ana iya hana bazuwar COVID-19, kuma kasar Sin za ta ci gaba da nuna himma da kwazo, domin ganin bayan ta a fadin duniya baki daya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China