Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana bata lokacin dakile annobar COVID-19
2020-03-10 20:07:40        cri
Tun bayan barkewar annobar numfashi ta COVID-19, an lura cewa, manyan kasashe biyu dake gabobi biyu na tekun Pasifik suna daukar matakan da suka sha bamban matuka.

Kasar Sin ta yi kokarin shawo kan annobar a cikin wata guda da wani abu. A ranar 9 ga wata, adadin mutane da aka tabbatar suka kamu da cutar a birnin Wuhan bai kai 20 ba, a sauran sassan kasar kuma, ba a samu rahoton sabon mutum da ya kamu da cutar ba a cikin kwanaki uku a jere, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana a jiya, an kusa ganin bayan annobar a kasar Sin.

Amma, a kasar Amurka, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar yana kara karuwa a kai a kai, inda ya zuwa karfe 7 na yammacin jiya, agogon gabashin kasar, an gano mutanen da suka kamu da cutar a jihohi 30 dake kasar. Goma daga cikinsu sun sanar da cewa sun shiga yanayi mai tsanani.

Bisa matsayinta na kasa mafi ci gaba a bangaren likitanci, bai kamata ba Amurka ta shiga irin wannan yanayi, saboda tun ranar 20 ga watan Janairun bana, an riga an gano mutum na farko da ya kamu da cutar a Amurka. Amma kafin kwanaki goma da suka gabata, gwamnatin kasar Amurka tana ganin cewa, babu hadarin kamuwa da cutar a Amurka.

Kwanan baya, tsohon mai ba da taimako ga sakataren harkokin wajen Amurka kan harkokin Asiya da tekun Pasifik Kurt Campbell, ya yi nuni da cewa, matakan da kasar Sin ta dauka sun samar da isasshen lokacin dakile annobar ga sauran kasashen duniya, amma ba tabbacin ko sauran kasashe suna yin aiki a kan lokaci.

Hakika jam'iyyu biyu na Amurka, suna yin cacar baka a kan batun ware kudi domin dakile annobar, ba tare da la'akari da moriyar al'ummun kasar ba, duk wadannan sun kawo illa ga aikin kandagarkin annobar a kasar.

Duk da cewa, kasashen duniya suna daukar matakai daban daban bisa tsarin kasashensu, da hakikanin yanayin da suke ciki, amma ya zama dole a mayar da rayukan jama'a a gaban komai, kuma bai dace a hada annoba da siyasa ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China