Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Magungunan gargajiyar Sin na taka rawar musamman wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-08 17:12:59        cri
Kafin shekaru biyar da suka gabata, kwararriya a fannin kimiyyar kasar Sin Tu Youyou wacce take nazarin magungunan sha na gargajiyar kasar Sin a cikin dogon lokaci ta yi nasarar tace sinadarin Artemisinin wato Qinghaosu, ta ceto rayukan jama'a wadanda suka kamu da cutar malariya sama da miliyan daya a fadin duniya, har ta samu lambar yabo ta Nobel, a halin yanzu yayin da ake kokarin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, magungunan sha na gargajiyar kasar Sin su ma suna taka rawar gani tare da magungunan kasashen yamma.

Misali likitocin kasar Sin sun hada wasu magungunan gargajiyar kasar Sin tare, domin kyautata gudanar aikin huhun mutanen da suka kamu da cutar, haka kuma sun samu sakamako a bayyane.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta tura likitocin gargajiyar kasar Sin sama da 5000 zuwa lardin Hubei, inda cutar ta fi kamari, har sun samar da magungunan sha na gargajiyar kasar ga mutanen da suka kamu da cutar kaso 75 bisa dari, a sauran sassan kasar kuwa, sun samar da magungunan ga mutanen da suka kamu da cutar kaso 90 bisa dari.

A ranar 6 ga wata, mambar tawagar ba da jagoranci kan aikin yakar cutar ta kwamitin tsakiya na JKS kuma mai kula da hukumar lafiya ta kasar Sin Yu Yanhong ta bayyana cewa, kawo yanzu mutanen da suka kamu da cutar sama da dubu 50 sun riga sun warke, yawancinsu sun taba shan magungunan gargajiyar kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China