Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar Taipei Da Amurka Ta Zartas Ba Ta Da Ma'ana
2020-03-09 16:44:24        cri

A wannan lokaci na musamman da kasashen duniya suke dukufa wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, wasu 'yan siyasan kasar Amurka suna neman majalisar dokokin kasar Amurka da ta sanya hannu kan dokar Taipei ta shekarar 2019, inda suka bukaci gwamnatin kasar Amurka da ta kara ko rage alakar dake tsakaninta da yankin Taiwan na kasar Sin kan harkokin siyasa, tsaro da diflomasiyya, bisa yadda sauran kasashen duniya suka daidaita dangantarkar dake tsakaninsu da yankin Taiwan na kasar Sin. Burinsu shi ne, hana bunkasuwar kasar Sin baki daya tare da kawo cikas ga yunkurin dunkulewar kasar Sin baki daya da amfani da wannan manufa wajen haifar da adawa tsakanin bangarorin zirin Taiwan na kasar, don kiyaye muradun kasar Amurka da bai dace ba kan harkokin kasa da kasa ta hanyar bata dangantakar tsakanin gwamnatin tsakiyar kasar Sin da gwamnatin yankin Taiwan na Sin.

Bayanai na nuna cewa, tun bayan Tsai Ing-wen ta hau kan mukamin jagorar yankin Taiwan, ya zuwa yanzu, akwai kasashe guda 7 da suka kashe dangantakar diflomasiyya tsakaninsu da yankin Taiwan, sun kuma kulla dangantakar diflomasiyya da jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. Lamarin da ya nuna cewa, manufar "kasar Sin kasa daya tak" ita ce ka'idar da jama'a da ma al'ummomin kasa da kasa suka yi na'am da ita.

Batun yankin Taiwan batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma batu ne da ya shafi muradun kasa. A shekarar 2018 da shekarar 2019, sassan da abin ya shafa da ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin da sauransu suka fitar da manufofin taimakawa yankin Taiwan, inda suka jaddada cewa, tabbas al'ummomi da kamfanonin yankin Taiwan za su sami damammakin raya harkokin yankin, wadannan manufofi kyawawan manufofin ne da za su taimaka matuka ga bunkasuwar yankin baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China