Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF zai samar da dalar Amurka biliyan 50 don tunkarar yaduwar COVID-19
2020-03-05 13:23:30        cri

Jiya Laraba, a yayin taron manema labarai da aka kira a birnin Washington na kasar Amurka, shugabar Asusun ba da lamuni na IMF Kristalina Georgieva, ta sanar da cewa, IMF zai samar da dalar Amurka har biliyan 50, domin ba da taimako ga mambobinsa wajen tunkarar cutar numfashi ta COVID-19.

Haka kuma, ta ce, za a samar da kudin ta hanyar tanadin kudaden gaggawa ga kasashen da ba sa samu kudin shiga da yawa ba, da kasashen dake samun saurin karuwar tattalin arziki cikin sauri. Kana, akwai dalar Amurka biliyan 10 dake cikin wadannan biliyan 50, da za a samar wa kasashe mafiya fama da talauci, ta hanyar ba su rancen kudi ba tare da karbar kudin ruwa ba.

Ta kuma kara da cewa, ko da yake a halin yanzu, halin da kasar Sin take ciki ya samu kyautatuwa, kuma kamfanoni da masana'antun kasar sun fara komawa bakin aiki bi da bi, amma, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a sauran kasashen duniya, ta haddasa kalubaloli gare mu. Yanzu haka, kashi 1 bisa 3 na mambobin IMF, sun tabbatar da cewa, akwai masu kamuwa da cutar cikin kasashensu, kuma bisa hasashen da aka yi, an ce, adadin karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2020, ba zai kai na shekarar 2019 da ta gabata ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China