Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta gamsu da karuwar mata masu samun damar ilimi sai dai suna fuskantar cin zarafi
2020-03-05 11:22:02        cri

Wani rahoto da asusun yara na MDD ya fitar a jiya Laraba, da hadin gwiwar shirin kyautata rayuwar mata na MDD, da shirin "Plan International", ya nuna ci gaba da aka samu a fannin ilimin mata cikin shekaru 25 da suka gabata, to sai dai kuma rahoton ya ce mata da 'yan mata, na ci gaba da fuskantar tsangwama a sassan duniya daban daban.

Rahoton wanda aka fitar gabanin taro na 64 dake tafe cikin mako mai zuwa, wanda zai maida hankali ga harkokin da suka shafi mata, ya nuna raguwar 'yan mata da ba sa zuwa makaranta da kusan mutane miliyan 79 cikin shekaru 20 da suka gabata, kana cikin shekaru 10 da suka gabata, 'yan mata da dama sun samu karin zarafin kaiwa matakin sakandare, sama da irin damar da takwarorin su yara maza ke samu.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, 'yan mata na fuskantar kalubale a mataki na karatun firamare, inda yawan yara matan da ba sa zuwa makarantun firamare ya kai miliyan 5.5 sama da takwarorin su yara maza a sassan duniya daban daban. Kuma ba a samu ci gaba ba a fannin rage yawan yara maza da mata da ba sa zuwa makarantun firamare tun daga shekarar 2007.

Har ila yau, rahoton wanda ya tattara bayanai na shekaru 25 game da yara mata, ya ce akwai kusan yara mata biliyan 1.1 dake rayuwa a sassan duniya daban daban.

Yayin taron tsara manufofi na aiwatarwa game da ci gaban mata da ya gudana a shekarar 1995, an fitar da cikakkun ka'idojin samar da daidaiton jinsi, wanda ya tanadi dabarun kawo karshen nunawa mata da 'yan mata wariya. To sai dai kuma bayan shekaru 25, nuna wariya da tsangwama ga jinsin mata na ci gaba da zama ruwan dare.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China