Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Xinjiang ya samu gagarumar nasara a fannoni uku
2020-01-14 10:22:39        cri

Hukumomi a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, sun bayyana cewa, yankin ya cimma gagarumar nasara a yaki da talauci da gurbatar muhalli da magance manyan hadurra a fannin harkokin kudi.

Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2019, yankin ya yi nasarar fitar da gundumomi 12 daga kangin talauci, daga kaso 6.1 cikin 100 a shekarar 2018 zuwa kaso 1.2 cikin 100 a shekarar da ta gabata. Haka kuma rukunin iyalai 9,355 na karshe dake zaune a gidaje masu hadari, sun kaura zuwa sabbin gidaje da aka gina musu.

A halin da ake ciki kuma, yanayin muhallin yankin na Xinjiang, shi ma ya inganta. A shekarar da ta gabata, hukumomi sun haramta amfani da makamashin dake gurbata muhalli da ma hana kamfanoni masu fitar da abubuwan masu gurbata muhalli yin aiki a yankin. Sannan a shekarar da ta gabata, matsakaicin ranakun iskar shaka mai kyau a manyan biraren jihar, ya karu zuwa kaso 1.5 kan makamancin shekarar 2018, yayin da ingancin ruwan kogi shi ma ya karu da kaso 1.2 cikin 100.

A shekarar 2019, kananan hukumomin jihar sun ba da rahoton haramta karbar rance ba bisa ka'ida ba, matakin da ya hana su shiga matsalar kudi. Haka kuma, gwamnatin yankin ta karfafa ba da rance ga sana'o'in kera kaya da ba da hidima.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China