Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kada a yi fuska biyu kan batun yaki da ta'addanci
2020-03-06 11:07:39        cri

Jiya Alhamsi, a yayin taro karo na 43 na kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD an kira wata muhawara da wakilai na musamman, masu sa kaimi ga kare hakkin Bil Adama a fannin yaki da ta'addanci.

Wakiliyar kasar Sin ta musamman kan batun kare hakkin Bil Adama Madam Liu Hua ta nuna cewa, ta'addanci na kiyayya ga daukacin Bil Adama, kuma a halin yauzu, ana fuskantar yanayi mai tsanani wajen yaki da ta'addanci a duniya. Har ma kungiyoyin ta'addanci suna sake kunnon kai a duniya, abin da ya kawo babbar barazana ga tsaron kasa da kasa, da ma shiyya-shiyya.

Taron ya kuma nuna cewa, kamata ya yi, kasashen duniya su hada kansu don yaki da ta'addanci tare, bisa ka'idoji da kuma tanade-tanaden tsarin mulkin MDD, da kuma sauran manufofi, da dokoki masu nasaba da dangantakar kasa da kasa.

Liu Hua ta nanata cewa, ta'addanci babu komai a ciki sai illata dukkanin duniya baki daya, hakan ya sa, bai kamata a yi fuska biyu kan batun yaki da ta'addanci ba. Sin na fatan hadin kai da bangarori masu ruwa da tsaki don dakile ta'addanci, tare da kiyaye tsaro da kuma zaman lafiyar kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, bisa ka'idar mutunta juna da hadin kai cikin adalci da daidaito. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China