Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Bai dace a amince da jita-jita da ke bazawa kan COVID-19 ba
2020-02-21 20:47:01        cri

A ranar 20 ga wata, agogon Geneva, hukumar lafiya ta duniya ta kira taron ganawa da manema labarai domin yin bayani kan yanayin da ake ciki wajen dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda babban jami'in kungiyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, bai dace a rika amincewa da jita-jita marasa tushe da ake bazawa ba, yanzu haka fitattun lokitocin kasa da kasa suna gudanar da aiki a kasar Sin, domin neman bakin zaren hana yaduwar kwayar cutar tare da lokitocin kasar Sin.

Jami'in ya kara da cewa, yanzu haka wasu na ta baza jita-jita marasa tushe, a don haka dole ne a mai da hankali kan wannan batun, bai kamata a amince da wannan jita-jita ba, kwararrun da abin ya shafa suna nazarin hanyoyin yaduwar kwayar cutar, kuma suna nazarin matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka domin ganin bayan annobar.

Ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta himmatu matuka domin hana yaduwar annobar, kokarinta ya taimakawa sauran kasashen duniya wajen daukar matakan da suka dace a kan lokaci, a don haka, ya kamata kasashen duniya su yi amfani da wannan dama, ta yadda za a hana kara bazuwar kwayar cutar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China