Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: COVID 19 ba cuta ce da ta yi matukar yaduwa a duniya ba
2020-02-25 19:26:40        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya jaddada a jiya Litinin cewa, ko da yake yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasashen Italiya, da Iran, da kuma Koriya ta kudu ya karu matuka, wanda hakan ya jawo hankalin al'umma sosai, a hannu guda wannan cuta, ba ta zama annoba dake matukar yaduwa a sassan duniya ba.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi wannan tsokaci ne a gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, ya kuma ce ya zuwa yanzu, wannan annoba ba ta yi gagarumar yaduwa a duniya ba, ana kuma iya sarrafa ta, kuma wadanda suke cikin yanayi na rai kwakwai mutu kwakwai, da kuma wadanda suka rasu sakamakon cutar, ba su da yawa a duk tsawon lokacin bullar ta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China