Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jiragen saman Habasha na ci gaba da jigila zuwa Sin
2020-02-28 11:18:05        cri
Jirgin saman dakon kaya na kasar Habasha, dauke da kayayyakin kiwon lafiya ton 50, ya sauka a birnin Guangzhou na kudancin kasar Sin, wanda ya zama jigila ta 24 da jirgin dakon kayan kasar ya yi zuwa Sin tun bayan barkewar cutar COVID 19.

Daga ranar 24 ga watan Junairu zuwa yanzu, jiragen sun yi jigilar ton 1,400 na kayayyakin kariya da dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar Sin.

Kamfanin jiragen ya dauki managartan matakan kare matuka da fasinjojinsa, bisa matakan da hukumar lafiya ta duniya ta tsara.

Manajan kula da zirga-zirga da cinikayya na kamfanin jiragen a birnin Guangzhou, Mehari Assefa, ya ce kamfanin jiragen sama na Habasha na da kyakkyawar dangantaka da kasar Sin, hatta a muhimmin lokaci irin wannan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China