Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha da Eritrea na neman zurfafa mu'amalar tattalin arziki bayan dinke barakar kasashen
2019-12-27 11:00:35        cri
Shugabannin kasashen Habasha da Eritrea sun sha alwashin zurfafa dangantakarsu bayan kasashen biyu sun yi nazarin fadada mu'amalar tattalin arziki a tsakaninsu.

Wannan mataki ya biyo bayan ziyarar da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya kai kasar Habasha a ranar Alhamis, wanda ya samu tarbar firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, inda suka jagoranci aza harsashin gina sabon ofishin jakadancin kasar Eritrea a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Shugaban kasar ta Eritrea ya lashi takobin yin aiki tare da bangaren Habasha domin farfado da muhimman damammaki da aka tafka hasararsu a cikin gwamman shekaru da nufin bude sabon babi game da huldar dake tsakanin kasashen biyu, ministan yada labaran kasar Eritrea, Yemane Gebremeskel, shi ne ya sanar da manufar ta shugaba Afwerki a lokacin bikin aza harsashin.

A nasa bangaren, firaministan kasar Habasha ya nanata cewa, gina sabon ofishin jakadancin Eritrea zai kara kyautata huldar diflomasiyyar dake tsakanin kasashen biyu, kamar yadda gidan radiyon kasar (FBC) ya raiwato firaminista Ahmed yana tabbatar da hakan.

Ahmed Abey ya ce, shekarar 2020, za ta kasance shekarar da za'a kafa tubulin kyakkyawar makoma ga cigaban alummomin kasashen Habasha da Eritrea har ma da shiyyar gabashin Afrika baki daya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China