Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nemi kasashen duniya su taimakawa yanayin dumamar siyasa a Guinea Bissau
2020-02-15 15:40:23        cri
Jakadiyar MDD a kasar Guinea Bissau, Rosine Sori-Coulibaly, ta nemi kasashen duniya su taimakawa kasar ta yammacin Afrika, yayin da take tsaka da fama da dumamar yanayin siyasa.

Jakadiyar wadda ita ce wakiliyar Sakatare Janar na MDD ta musammam kuma shugabar ofishin Majalisar mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, ta lura da sabon tankiyar da ta kunno kai tsakanin masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasa, wadda ke tarnaki ga zaman lafiya da kokarin gwamnatin kasar na mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki da inganta zamantakewar al'umma.

Domingos Simoes Pereira, wanda ke jagorantar zagaye na farko na zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 24 ga watan Nuwamba, ya sha kaye a hannun Umaro Sissoco Embalo, a zagaye na biyu na zaben da aka yi a ranar 29 ga watan Disamban bara. Kuma kawo yanzu, Domingos Pereira, ya ki amincewa da kayen da ya sha, inda yake kalubalantar sakamakon zaben.

Rosine Sori-Coulibaly, ta bayyanawa kwamitin sulhu na MDD a jiya cewa, har yanzu ba a warware batun a shari'ance ba, domin bada dama ga mika mulki karon farko cikin kwanciyar hankali a kasar, ga shugaban kasar da aka zaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China