Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta ce raguwar amfani da albarkatu na kara tsananta yanayin jin kai a Somalia
2019-08-13 10:35:33        cri

Tarayyar Afrika AU, ta ce raguwar al'ummomi wajen amfani da albarkatun dake akwai, na ba da gudunmuwa ga kara tabarbarewar yanayin jin kai da ake ciki a sassa daban-daban na Somalia.

A cikin rahoton da ta fitar jiya, AU ta alakanta kalubalen da da ake fuskanta na samar da ayyukan jin kai a sassan Somalia da raguwar amfani da albarkatu daga al'ummomi da kuma wariya da tsangwamar da ake yi wa wasu a cikin al'umma.

Tarayyar ta jaddada cewa, shirinta na AMISOM mai wanzar da zaman lafiya a kasar, ya samar da tsaron da ake bukata na ba da agajin jin kai, kuma ya taimaka wajen samar da nagartattun dabarun kare fararen hula.

Rahoton ya kara da cewa, kafa tawagogin fararen hula karkashin AMISOM ya saukaka samun damar isa ga mutane mafi rauni a sassan kasar.

Har ila yau, AU ta ce kara hada hannu tsakaninta da MDD da gwamnatin Somalia da sauran masu ba da gudunmuwa na kasa da kasa, ya taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa da ayyukan inganta zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali da samar da maslaha a Somalia. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China