Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kada Amurka ta tsoma baki cikin harkokin gidanta
2019-12-30 19:34:24        cri

Game da tsokacin da wasu Amurkawa suka yi kan yanayin yaki da ta'addacin da jihar Xinjiang ta kasar Sin ke aiwatarwa, a yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, tsokacin an gina shi ne bisa jita-jita maras tushe, kuma kasar Sin tana fatan Amurka za ta daina tsoma baki a cikin harkokin gidanta, in ba haka ba, illar hakan za ta koma kan su.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi yau, jami'in ya bayyana cewa, yanzu tattalin arzikin jihar Xinjiang yana ci gaba da samun bunkasuwa, kuma zamantakewar al'ummar jihar ita ma tana cikin yanayin kwanciyar hankali, kana rayuwar al'ummar jihar tana kara kyautatuwa a kai a kai. Ban da haka kuma, al'ummun jihar suna jin dadin al'adu masu kunshe da wadata, da addini cikin 'yanci.

Ana iya cewa, a cikin shekaru sama da 60 da suka gabata, wato tun bayan da aka 'yantar da jihar cikin lumana, gwamnatin jihar tana gudanar da harkokinta yadda ya kamata, ko ta fuskar ci gaban tattalin arziki, ko ta fuskar raya al'adun gargajiya, ko kuma ta fuskar jituwar zamantakewar al'umma.

To sai dai kuma a nata bangare, Amurka ta yi watsi da hakikanin yanayin da jihar ke ciki, inda sau tari ta rika yin karya domin shafawa kasar Sin kashin kaji. A game da haka ne kuma kasar Sin, ke fatan Amurka za ta daina yin hakan.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China