Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta soke takardun iznin aikin 'yan jaridar the Wall Street Journal da ke Beijing
2020-02-19 19:26:59        cri

A ranar 3 ga watan Fabrairun bana, Jaridar the Wall Street Journal ta wallafa sharhin da Furofesa Walter Russell Mead na Kwalejin Bard ta kasar Amurka ya rubuta, inda ya zargi kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta ke yi na yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Ban da wannan kuma, babban editan jaridar ya sanya sharhin wani kai mai ban tsoro matuka, lamarin da ya fusata jama'ar Sin da ma suka daga kasashen duniya.

Game da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang ya furta cewa, bangaren Sin ya nuna wa Jaridar rashin jin dadinsa, inda ya bayyana ra'ayin Sin na bukatar jaridar da ta amince da kuskuren da ta yi, ta kuma nemi gafara da ma hukunta wadanda suka aika wannan danyen aiki. Amma abin bakin ciki shi ne, kawo yanzu jaridar tana ta neman hujja da ma daina neman gafara, sannan ba ta hukunta wadanda abin ya shafa ba.

Geng Shuang ya jaddada cewa, ko da yaushe Sin na kula da harkokin 'yan jaridar ketare bisa doka. Game da kafofin watsa labarai na kasashen waje da ke watsa kalaman nuna bambancin launin fata, da ma shafa wa Sin kashin kaza, jama'ar Sin ba sa marhabin da su. Sakamako haka, Sin ta tsai da kudurin soke takardun iznin yin aiki da ta bai wa 'yan jaridar the Wall Street Journal guda uku da ke birnin Beijing tun daga yau.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China