![]() |
|
2019-12-13 20:12:28 cri |
Kwanan baya mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin Asiya da tekun Pasifik David Stilwell ya gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, Amurka ta taimaka matuka ga ci gaban kasar Sin a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, amma kasar Sin ba ta gode mata ba, a don haka Amurka ba ta ji dadi ba, kan wannan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana yau cewa, tsokacinsa ba shi da tushe ko kadan.
Madam Hua ta kara da cewa, David Stilwell ya sha bayyana taimakon da Amurka ta baiwa kasar Sin, amma kasar Sin ba ta amince da ra'ayinsa ba.
Hua Chunying ta jaddada cewa, Sin da Amurka suna gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu ne bisa tushen moriyar juna, Amurka ita ma ta samu moriya daga hadin gwiwar, don haka ya dace Amurka ta fahinci saurin ci gaban kasar Sin.
Hua ta ci gaba da cewa, kasar Sin ta sake bukatar Amurka da ta kawar da ra'ayin da bai dace ba, ta daidaita huldar dake tsakaninta da kasar Sin ta hanyar da ta dace, haka kuma ta daina tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin, tare kuma da daina shafawa kasar Sin kashin kaza, ta yadda za a ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China